Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Ziyarci Fasinjojin Jirgin Kasa Da Aka Sako A Asibitin Kaduna.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da fasinjoji 23 da aka sako daga harin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna, a ranar 28 ga Maris na wannan shekarar, a asibitin makarantar horas da sojoji ta kasa (NDA) da ke Kaduna.

Shugaban ya kai ziyarar bazata asibitin domin ganin wadanda harin jirgin kasa ya rutsa da su, bayan kaddamar da rukuni na 69 na daliban makarantar ta NDA da za su sami rohon soji, a Afaka, jihar Kaduna.

Shugaba Buhari ya godewa sojojin Najeriya bisa jajircewar da suka yi wajen ganin an kubutar da mutanen da aka yi garkuwa da su daga hannun ‘yan ta’addan Boko Haram.

Wakilan kwamatin daukar mataki na babban hafsan hafsoshin tsaro karkashin jagorancin Manjo Janar Usman Abdulkadir mai ritaya, wanda ya taimaka wajen sako fasinjojin ne suka yi rakiyar shugaban kasar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *