Mai Martaba Sarkin Kano: limintar da ‘yaya wajibi ne akan iyaye.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya jaddada bukatar Gwamnatotci a matakai uku su cigaba da taimakawa ilimin addini dana zamani.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci hakan ne lokacin day a jagoranci bikin yaye dalibai da suka sauke karatun Alquu’ani mai Tsarki na Makarantar koyar da Alkur’ani ta Malam Falalu Haido kake Unguwar Fagge a yankin Karamar Hukumar Fagge a Kano.

Sarkin wanda ya yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa yadda take tallafawa harkokin ilimi a bangarori daban daban.

Yayi kira ga iyaye su cigaba da sa ido sosai wajen tarbiyar ‘yayansu, inda yace ilimintar da “yaya wajibi ne akan iyaye, Sarkin ya kuma yi kira ga iyayen su dungayi kokarin sauke nauyin dake kansu ta hanyar biyan kudaden makarantar “yayansu.

Mai Martaba Sarkin kazalika yaja hankalin Malaman makarantar su rike Amanar da aka dora musu wajan baiwa yaran ilimi mai inganci tareda cusa musu tsoron Allah, inda ya bgodewa Malaman Makarantar bisa yadda suka koyar da daliban har suka samu dammar sauke Alqur’ani mai tsarki.

Alhaji Aminu Bayero daganan sai yayi kira ga daliban su cigaba da neman ilimi domin zurfafa karatunsu, tareda kira ga al’uma da a cigaba dayin addu’oin samun zaman lafiya da saukin rayuwa baki daya.

Abubukar Balarabe Kofar Naisa

Chief Press Secretary Kano Emirate Council.

05/10/2022

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *