Sama da fursunoni 40 da suka tsere daga gidan yarin Kuje ne har yanzu ba a gano su ba

Akalla fursunoni 422 da suka tsere daga gidan yarin Kuje da ke Abuja a ranar 5 ga Yuli, 2022, har yanzu ba a kama su ba, in ji rahotanni

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa fursunoni 879 da suka hada da manyan ‘yan ta’addan Boko Haram 64 ne suka tsere daga gidan yarin.

Kakakin hukumar ‘yan sandan Najeriya Umar Abubakar, ya ce mutane biyar da suka hada da jami’in tsaron farin kaya na Najeriya da kuma wasu fursunoni hudu sun mutu a harin.

Sa’o’i kadan bayan haka, kungiyar ‘yan ta’adda ta Da’esh a yammacin Afirka ta dauki alhakin kai harin.

A ranar 14 ga watan Yuli ne dai jaridar PUNCH ta bayar da rahoton cewa kwamitin majalisar wakilai mai kula da aikin gyaran hali ya ce hukumar ta NCoS ta kama fursunoni 421 kuma ba a gano sauran 454 har yanzu ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *