Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabon Shugaban da zai jagoranci ragamar NSIA a Najeriya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Aminu Umar-Sadiq a matsayin sabon shugaban hukumar nan ta NSIA ta kasa.

Wani rahoto da The Cable ta fitar a ranar Litinin ya tabbatar da cewa Aminu Umar-Sadiq zai karbi ragamar hukumar daga hannun Mista Uche Orji.

Wa’adin Uche Orji ya cika a karshen Satumban 2022 domin ya rike wannan mukami a hukumar NSIA sau biyu daga Oktoban 2012 zuwa yanzu.

Baya ga haka, gwamnatin tarayya ta amince da nadin Kolawole Owodunni da Bisi Makoju a matsayin manyan darektoci a wannan hukumar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *