Yadda Likita Ya Binne Wata Mata A Babban Asibitin Kwara

Jami’an bincike a jihar Kwara sun gano gawar wata mata da aka binne a ofishin babban daraktan asibitin Kaiama, Dr Abbass Adeyemi.

An tsinci gawar matar mai suna Nofisat Halidu a wani kabari mara zurfi a asibitin a gaban mijinta, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.

Adeyemi, wanda a halin yanzu yake tsare a hannun ‘yan sanda, an alakanta shi da laifuka daban-daban na kisan kai.

A watan da ya gabata ne rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta kama Adeyemi kan kashe wani direba mai suna Emmanuel Yobo Agbovinuere.

Wanda ake zargin ya fito daga karamar hukumar Offa ta jihar Kwara, ana zargin shi da kashe direban a ranar 3 ga watan Satumba a garin Benin tare da jefar da gawarsa a unguwar Otofure da ke kan hanyar Benin zuwa Legas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *