Tinubu ya bayyana Aisha Buhari a matsayin shugabar tawagar yakin neman zaben APC na mata.

A ranar Asabar ne jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta bayyana uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari a matsayin shugabar tawagar yakin neman zaben ta na mata.

Sauran wadanda zasu taka rawar gani sun hada da Sanata Oluremi Tinubu, Sanata mai wakiltan Legas ta tsakiya a zauren majalisar dattawa na wa’adi 3 a majalisar dattawa kuma matan tsohon gwamnan jihar Legas da kuma Nana Shettima, uwargidan dan takarar mataimakin jam’iyyar APC

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Rinsola Abiola, diyar marigayi Cif MKO Abiola, kuma jigo a jam’iyyar APC, ta fitar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *