Sarkin Kano ya ja hankalin Matasa da ‘yan siyasa su gujewa dukkannin abunda zai tada hankalin al’umma a lokutan yakin neman zabe

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yaja Hankalin al’umma da yan siyasa su rika yin kalamai masu inganci a cikin al’umma

Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da ya jagoranci gudanar da addu’oi na musamman domin samun zaman lafiya ga kasa baki daya wadda aka gudanar a babban masallacin juma’a dake cikin birnin Kano.

Alhaji Aminu Ado Bayero yace ya shirya wannan addu’a ne domin yiwa kasa addu’a da kuma zabuka da suke tunkararmu a shekara 2023.

Mai martaba sarkin kazalika yayi kira ga Matasa su gujewa dukkan abinda zai kawo fitina a lokutan yakin neman zabe.

Sarkin ya bukaci Al’umma su zama masu Ladabi da biyayya da tausasa harshinansu.

Yayi fatan dukkan yan Siyasa zasu karbi shawarwari da Malamai suke bayarwa na suyi yakin neman zabe cikin nutsuwa ba tareda wani tashin hankali ba.

Daganan kuma Mai Martaba Sarkin na Kano Alhaji Aminu Ado Bayero yace shirya adduoin yazo dai dai lokacin da ake bikin cikar Najeriya shekara 62 da samun yancin kai.

Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Chief Press Secretary to Kano Emirate Council.
10/10/2022

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *