Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya halarci taron murnar cika Shekara 62 da samun yancin kan Najeriya.

Taron an gudanar dashi ne a filin wasan kwallon kafa na Sani Abacha dake kofar Mata a cikin birnin Kano bisa jagorancin Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje Khadimul Islam.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero wanda shine Shugaban Majalisar Sarakunan Kano ya kasance a wajan taron tareda Masu Martaba Sarakunan Bichi da Rano da Gaya da Kuma Karaye.

An dai Gudanar da taron ne tareda da faretin ban girma daga Jami’an “Yan Sanda dana hana fasakori dana hana shige da fice da kuma na kula da gidajen gyaran hali.

Sauran jami’an da suka gudanar da faretin sun hadar dana kula da ababan Hawa ta jihar Kano da sauran kungiyoyin addini da Yan makaranta.

Abubakar Balarabe Kofar Naisa
Chief Press Secretary to Kano Emirate Council.
01/10/2022

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *