Kotu Ta Daure “Mama Boko” Haram Da Wasu Mutane Tsawon Shekaru 7 A Gidan Yari.

Kotu ta yanke hukuncin dauri ga Aisha Alkali Wakil, (aka Mama Boko Haram) tare da Tahiru Alhaji, Saidu Daura da kuma Yarima Lawal Shoyode.

Mai shari’a Aisha Kumaliya ta babbar kotun jihar Borno, ta yanke musu hukuncin daurin shekaru bakwai a ranar Alhamis, 29 ga watan Satumba, 2022, bisa samunsu da laifin hada baki su aikata laifuka da kuma wasu shekaru 7 na karbar kudin haram.

Kafin a yanke musu hukunci, an fara gurfanar da wadanda ake tuhumar ne a ranar 14 ga Satumba, 2020 a gaban Mai shari’a Kumaliya bisa tuhume-tuhume biyu na laifukan hada baki da kuma karbar kudi ta hanyar karya ta N15,000,000.00 (Naira Miliyan Goma Sha Biyar).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *