Sanata Uba Sani Ya Halarci Taron Ƙaddamar Da Littafi A Saminaka, Ya Sayi Kwafin Littafin Miliyan 10

Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Kaduna a Jam’iyyar APC Sanata Uba Sani Ya kaddamar da wani littafi a Ƙaramar Hukumar Saminaka dake Jihar, inda ya sanar da sayen littafin akan kuɗi Naira Miliyan Goma ga mawallafin sa.

Sanata Uba Sani ya sanar da hakan a cikin wani saƙo daya fitar ga Manema labaru

“A yau, na ji daɗin kasancewa Babban Mai Gabatarwa kuma Mai ƙaddamar da littafin mai suna: “Fundamentals Of Geoscience” na ɗan’uwana kuma abokina, Farfesa Matoh Dary Dogara wanda na san shi kuma na yi aiki da shi tsawon shekaru da dama”

A cewar Uba Sani, wannan taro wanda ya samu halartar wasu fitattun mutane daga jihar Kaduna da wajenta, ya ƙunshi Malaman Jami’o’i daga sassan kasar nan ya ba shi damar yin magana kan mahimmancin ilimin kimiyyar kasa, da ya shafi muhalli.

Ya kuma yabawa wanda ya rubuta littafin, inda yace babu shakka yana ɗaya daga cikin haziƙan masu hankali da suka fito daga jihar Kaduna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *