Jigon APC: Tinubu ya tafi Landan ne saboda mutane ba za su bar shi ya huta ba a Legas.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya tafi Landan don ya huta inji wani dan majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Ayo Oyalowo.

Rashin halartar Tinubu a yarjejeniyar zaman lafiyar da aka yi a ranar Alhamis ya janyo ce-ce-ku-ce, inda aka rika yada jita-jitar cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki ba shi da lafiya.

Amma da yake magana a wani shirin gidan talabijin na ARISE, Oyalowo ya ce, “Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yana Landan,
saboda ba zai iya hutawa a Legas ba”.

Yace Tinubu yana aiki kusan sa’o’i 20 a cikin sa’o’i 24 a kowace rana, don haka masu kusa da shi sun shawarci shi ya bar kasar saboda ya samu daman hutawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *