Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Damaturu, babban birnin jihar Yobe, ta bayyana Bashir Sheriff Machina a matsayin dan takarar Sanatan Yobe ta Arewa na jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa.
Kotun ta kuma umurci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta buga sunansa a matsayin dan takarar.
Alkalin kotun, Mai shari’a Fadima Aminu ta bayar da wannan umarni ne a ranar Laraba a Damaturu, babban birnin Yobe.
Alkalin kotun ya tabbatar da cewa Machina an zabe shi bisa gaskiya kuma ya zama dan takarar sanatan Yobe ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC a zaben fidda gwani na jam’iyyar a ranar 28 ga watan Mayu.
Karin Bayani na nan tafe….