Sojoji Sun Kubutar Da Wata Mata, ‘Ya’yanta 4 A Kaduna

Dakarun rundunar ‘Operation Forest Sanity’ sun ceto wata mata da aka yi garkuwa da ‘ya’yanta hudu tare da wasu mutanen kauyen guda uku a wani sintiri a kananan hukumomin Birnin Gwari da Chikun.

An tattaro cewa sojojin sun fuskanci luguden wuta daga ‘yan bindigar a lokacin da suke sintiri a kan titin Birnin Gwari-Gayam-Kuriga-Manini.

Aminiya ta gano cewa sojojin sun mayar da martanin hari inda suka yi nasarar fatattakar ‘yan bindigar suka tsere zuwa cikin dazuzzuka kuma suka bar wadanda suka yi garkuwa da su a hannunsu.

Samuel Aruwan, kwamishinan ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida a jihar ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Ya ce wadanda aka ceto sun hada da – Gloria Shedrack da ‘ya’yanta hudu masu suna Jimre Shedrack, Jonathan Shedrack, Angelina Shedrack da Abigail Shedrack. Daga cikin manya da aka kubutar dasu kuma sun hada da Joseph Ishaku da John Bulus.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *