Ambaliyar Ruwa Ta Lalata Babban Titin Lokoja, Gidajen Ruwa, Cibiyoyin Bauta

Masu ababen hawa da ke bin hanyar Lokoja-Ajaokuta, wadda ta hada wani bangare na gabacin jihar, sun makale a titin Ganaja zuwa Lokoja a ranar Litinin din da ta gabata, yayin da ruwa daga kogin Neja/Benue ya mamaye titin tare da sa ba za a iya wucewa ba.

An tattaro a ranar litinin cewa motoci guda uku da suka yi yunkurin tsallakawa sun makale a kan babbar hanyar, inda wasu suka yi fakin a kan titin tare da haddasa doguwar layukan motocin da aka ajiye a gefen hanya.

Wani direban mota mai suna Malam Idris Usman wanda ya yi ikirarin cewa yana tuka Ayangba -Lokoja a kowace rana, ya ce sai da ya sauke fasinjojinsa a kauyen Ganaja-Lokoja sannan ya koma.

An lura cewa masu ababen hawa da za su je Gabas daga Arewa sai sun bi ta Okene -Adogo ta babbar hanyar Ajaokuta zuwa Itobe don ci gaba da tafiye-tafiyensu.

Fasinjoji da dama ne suka hau kwalekwale domin wucewa ta bangaren babbar hanyar zuwa daya bangaren Lokoja domin ci gaba da tafiya.

Har ila yau, gidaje da dama a rukunin Gadumo, Adankolo, Kpata da Marines da ke Lokoja da majami’u, masallatai da wuraren kasuwanci ne ambaliyar ta rutsa da su.

A halin da ake ciki, Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) ta ce akalla mutane 18,406 ne ambaliyar ruwa ta raba da muhallansu a kananan hukumomi 14 na jihar.

Darakta Janar na hukumar Yabawa Kolo ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Maiduguri ranar Litinin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *