Ku bude jami’o’i a ci gaba da karatu, gwamnatin tarrayya ta umurci shugabanin jami’o’i.

Gwamnatin tarayya ta umurci shugabannin jami’o’in da su sake bude jami’o’i tare da ci gaba da karatu.

A tabbatar da cewa ‘yan kungiyar ASUU sun koma bakin aiki da gaggawa tare da ci gaba da al’amuran yau da kullum a harabar jami’o’i daban-daban na kasar.

Daraktan kudi da asusu na NUC, Sam Onazi ne ya bayyana haka a cikin wata wasika da ya aika a madadin babban sakataren hukumar Abubakar Rasheed.

An rufe jami’o’in gwamnati a kasar tun ranar 14 ga Fabrairu, 2022 lokacin da membobin kungiyar Ma’aikatan Ilimin Jami’o’i suka shiga yajin aikin domin nuna rashin jin dadi su kan wasu hakkokin da ba a biya ba.

A makon da ya gabata ne kotun masana’antu ta kasa (NIC) Abuja ta umurci malaman da su janye yajin aikin na watanni bakwai su koma ajujuwa amma daga bisani ASUU ta daukaka kara kan umarnin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *