Gwamnatin tarayya ta janye umarnin da yace shuganannin jami’o’i na su koma bakin aiki.

A wani rahoton da muka samo da sanyin safiyar yau, an wata wasika mai lamba NUC/ES/138/Vol.64/135 da kungiyar NUC ta fitar ta umarci shugabannin jami’o’in gwamnati a Najeriya da su bude makarantu tare da kiran dalibai su dawo makaranta.

Sai dai, a wata sabuwar wasika mai lamba NUC/ES/138/Vol.64/136, hukumar ta NUC ta janye batun, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Hukumar dai bata bayyana dalilin bayyana janye umarnin ba, ta dai ce daga baya za ta magantu akan duk wani ci gaba da aka samu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *