APC: Buhari ne ya bukaci a cire Osinbajo Daga Yakin Neman Zaben Tinubu

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta yi magana a kan cire sunan mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo daga cikin kwamitin yakin neman zaben Asiwaju Bola Tinubu, dan takararta na shugaban kasa a babban zaben 2023.

Rashin sunan Osinbajo da farko dai a jerin ‘yan kwamitin 422 ya jawo cece-kuce daban-daban.

Da yake bayyana dalilin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, Festus Keyamo, mai magana da yawun yakin neman zaben, ya ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci Osinbajo da Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya kada su kasance cikin kwamitin yakin neman zaben domin su mai da hankali wajen yin aikin su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *