Falana: ASUU Za Ta Daukaka Kara A Yau

A ranar Juma’a ne kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) za ta shigar da kara a gaban kotun daukaka kara da ke Abuja, domin ta ba da umarnin shiga tsakani tare da yin watsi da hukuncin da kotun masana’antu ta kasa ta yanke na janye yajin aiki da take da kuma Mambobin ta su koma bakin aiki.

Lauyan kungiyar ASUU kuma mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Mista Femi Falana, ya tabbatar da hakan a ranar Alhamis ga jaridar Tribune Online a wata tattaunawa da suka yi da ita.

Ya ce: “Dazun nan mun aika da wani kotu domin ya karbo sahihancin rahoton hukuncin kuma mu shirya domin ba mu damar shigar da bukatar mu na neman a yanke hukunci a yau Juma’a.”

“Duk da cewa muna da tagar kwanaki 14 don yin hakan, gobe da safe za mu shigar da takardar daukaka kara kuma abin da zan iya fada kenan a yanzu kan lamarin.”

Idan dai za a iya tunawa, gwamnatin tarayya ta kai ASUU gaban kotun masana’antu ta kasa inda ta bukaci ta tilasta wa kungiyar ta janye yajin aikin da ta kwashe watanni bakwai tana yi wanda ya durkusar da harkokin ilimi a jami’o’in gwamnatin kasar nan.

Sai dai kotun ta amince da rokon ne a ranar Laraba inda ta umurci malaman da su koma bakin aiki. ASUU ba ta gamsu da matsayin kotun ba, don haka ne ake son daukaka kara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *