Har Yanzu Buhari Bai Cika Alkawuran Da Yayi Yayin Da Yake Neman Takara -Tsohon Kakakin PDP

Tsohon Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar PDP na Kasa, Kola Ologbondiyan, yace Shugaban kasa Muhammadu bai cika alkawuran da yayi lokacin da yake neman takara shugabanci.

Ologbondiyan, wanda ya yi magana a gidan Talabijin na Channels TV’s Sunrise Daily ya ce abin dariya ne a yi maganar inganta tattalin arzikin Najeriya a karkashin gwamnatin yanzu.

Ya ce, “Manyan alkawurran guda uku da Buhari ya yi yakin neman zabe, duk sun zo daga sama har kasa, yanayin yaki da cin hanci da rashawa ko yaki da ta’addanci da inganta tattalin arzikin kasa, babu daya daga cikinsu da Buhari ya cimma.

“A karkashin gwamnatin APC an samu karin hanci da rashawa. Dole ne in fadi hakan a fili kuma ’yan Najeriya sun sani, a tarihin kasar nan, ba mu taba ganin cin hanci da rashawa ba kamar yadda muke gani a yau.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *