Al-Mustapha Yayi Kuka Kan Rashin Tsaro A Najeriya.

Hamza Al-Mustapha, tsohon babban jami’in tsaro (CSO) ga marigayi Janar Sani Abacha yayi kukan kuka babu kakkautawa kan halin tsaro a Najeriya.

Ya fashe da kuka a ranar Asabar a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar matan Kiristocin Arewa a gidansa da ke Abuja.

Abin da Najeriya ke bukata a yanzu shi ne shugabanci. Dole ne mu fita daga inda muke, mutane za su zo su yi amfani da addini su ce ‘Saboda shi Musulmi ne, ba zai iya zama wannan ba; saboda shi Kirista ne, ba zai iya zama wannan ba,” in ji dan takarar shugaban kasa na kungiyar Action Alliance (AA) a taron.

“Wadannan sinadarai ne da suka kashe Najeriya a baya wadanda kuma suke amfani da su wajen kashe Najeriya nan gaba.

Ba za mu yarda da hakan ba. Na zauna kusa da ku; ke kanwata ce. Daga cikinku akwai iyaye. Za mu mutu muna kare ku.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *