Wani dan China ya kashe budurwarsa ‘yar Kano a Unguwar Janbulo.

Wani dan kasar China ya yiwa wata budurwa ‘yar shekara 23 yankan rago, a unguwar Janbulo da ke karamar hukumar Gwale dake jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na daren ranar Juma’a bayan wanda ake zargin ya kawo wa marigayiyar ziyara mai suna Ummakulsum Sani Buhari a gidan iyayenta da ke kusa da ofishin Hukumar kula da muhalli ta gwamnatin tarayyar Najeriya NESREA.

Tuni dai aka kai wanda ake zargin zuwa ofishin ‘yan sanda da ke unguwar Dorayi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma yi alkawarin bayar da karin bayani nan bada jimawa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.