An amince Azman ya koma zirga-zirga

Hukumar kula da sufirin jiragen sama ta Najeriya ta saki lasisin zirga-zirgar jiragen sama (ATL) na kamfanin Azman, ta amince kamfanin ya ci gaba da ayyukansa.


Rahma ta gano cewa kamfanin jiragen sama na AZMAN sun dakatar da harkokin su na jigila a ranar Alhamis bayan NCAA ta ki sabunta lasisinsa na daukar fasinja (ATL) sakamakon basusuka da ake bin kamfanin wanda ya kai har biliyan 1.2.

Hukumar ta NCAA ta dakatar da sabunta lasisin na kamfanin jirgin don ba ta damar sanya hannu kan yarjejeniyar kan yadda za ta biya kudaden da ake bin su.

Sabon Lasisin da ke dauke da sa hannun Darakta-Janar na NCAA, Kyaftin Musa Nuhu ya ce:

“An ba da lasisin gudanar da ayyukan jigilar fasinjoji da kaya a ciki da wajen Najeriya, bisa ga sashe na 18.2.2.3 da 18.2. 2.4 na Dokokin Jirgin Sama na Najeriya 2015 zuwa ga:

AZMAN AIR SERVICES LIMITED 1, Zaria Road, Kano na tsawon shekaru biyar (5) Ranar fitowa: 16 ga Satumba, 2022 Ranar ƙarshe: 15th Satumba, 2027

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *