Shugaban Amurka Joe Biden, ya yi magana da Sarki Charles III a yau, in da ya masa ta’aziyya

Shugaban Amurka Joe Biden, ya yi magana da Sarki Charles III a yau, in da ya masa ta’aziyya da kuma shaida masa irin yadda Amurkawa ke matukar kaunar Sarauniya.

A cikin wata sanarwa da fadar gwamnatin Amurka ta fitar, ta ce shugaban ya tuna da irin kirki da kuma karramawar da Sarauniya ta yi musu shi da mai dakinsa a fadar Windsor Castle a watan Yunin da ya wuce.

Sanarwar ta ce darajar Sarauniya da mutuncinta su suka sa kawancen kasashen biyu ya yi karko har ma ya zama sanadin samar da wata dangantaka ta musamman tsakanin Burtaniya da Amurka.

Shugaban na Amurka zai halarci jana’izar Sarauniya da za ayi a Landan ranar Litinin mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *