Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya sun yi kira da a yi garambawul ga kundin tsarin mulki na 1999.

Gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya 19 da sarakunan gargajiya a yankin sun yi kira da a yi garambawul ga kundin tsarin mulki na 1999, don samar da yan sandan jihohi.

A cewarsu wannan ne kadai zai sa a shawo kan matsalar tsaro da yankin ke fama da ita dama kasa baki daya.


Yankin Arewacin na Najeriya ya jima yana fama da matsalar yan fashin daji, da satar mutane don neman kudin fansa, da sauran nau’o’in ayyukan ta’addanci.


Kungiyar gwamnonin arewa ta NGF, da ta sarakunan gargajiya (NTRC) sun aminta da hakan ne bayan kammala wani taro ranar Litinin a Abuja.


Wannan ne karon farko da kungiyoyin biyu suka cimma matsayar samar da yan sandan jihohi a taron hadin gwuiwa.


Sai dai akwai masu fargabar cewa wasu gwamnonin jihohin kan iya amfani da yan sandan da za a samar a karkashin ikonsu, don cin zarafin abokan adawa ko kuma cimma burinsu na siyasa.


An dade ana kiraye-kirayen samar da yan sandan jihohi, inda masu bukatar a yi hakan ke kafa hujjar cewa rundunar yan sanda ta kasa ta yi kadan, idan aka yi la’akari da girman matsalar tsaron da kasar ke fama da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *