Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) reshen jami’o’inta da su koma bakin aiki.

Gwamantin ta mika wannan bukatar ce a wata ganawa da ta yi da shugabannin ASUU na jami’ointa biyu a ranar Talata.


Taron wanda aka shafe awowi ana yi tsakanin bangarorin biyu, an tashi ba a cimma wata matsaya ba; Amma za a sake zama a mako mai zuwa — sai dai babu tabbacin haka.


Wakilinmu ya gano a  yayin zaman, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, Usman Bala Mohammed ya roki malaman jami’oin jihar da su koma bakin aiki, ko da za su dakatar da zama ’ya’yan kungiyar ne na watan uku.


Sai dai bangaren kungiyar ya ce hakan ba zai yiwu ba, domin ba za su iya tunkarar uwar kungiyar da wannan bukata ba.


A hirarsa da ’yan jaridu bayan taron, shugaban ma’aikatan jihar ya ce, babu wani mataki da za su dauka kan malaman jami’an a yanzu, amma idan tura ta kai bango za su san abin da za su yi.


A nasa bangaren Shugaban ASUU Reshen Jihar Kano, Abdulqadir Muhammad, ya ce, sun fada wa gwmnati gaskiya kan batun janyewa da kuma sake haduwa a mako mai zuwa; sai dai daga uwar kungiya idan wani abu ya taso”.

Leave a Reply

Your email address will not be published.