Kungiyar kwararrun likitoci ta Najeriya ta shaida cewar, akalla kwararrun likotoci 500 ne suka fice daga Najeriya domin kama aiki a wasu kasashen waje.

Kungiyar ta ce, likitocin da yawansu ma’aikatan gwamnatin jihohi ne da na tarayya.

Kamar yadda rahotanni ke cewar
Shugaban kungiyar, Dr Victor Makanjuola ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Benin yayin da yake amsa tambayoyi kan taron kungiyar na shekara-shekara da aka gudanar.

Ya ta’allaka laifin ficewar likitoci daga Najeriya ga gwamnatin kasar, inda yace sam gwamnati bata ba da cikakkiyar kulawa ga bangaren lafiya da kuma kula da jin dadin ma’aikata har ma da mutunta su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *