Gwamnatin tarayyar ta gurfanar da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) a gaban kotun ma’aikata.

Gwamnatin tarayyar ta gurfanar da kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) a gaban kotun ma’aikata game da yakin aikin da suka kwashe wata bakwai suna yi.


A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar kwadago ta kasar, Olajide Oshundun, ya fitar a karshen makon nan ya ce gwamnati ta dauki mataki ne bayan tattaunawa tsakaninta da kungiyar malaman jami’o’in ta ci tura.


Gwamnati tana son kotun ma’aikatan ta bai wa mambobin ASUU umarnin su koma bakin aiki, a yayin da ake ci gaba da shari’a a kan batun.
Ana sa rai kotun za ta soma sauraren karar a yau Litinin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *