Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu, wacce ita ce sarauniya mafi tsufa a duniya ta rasu a cewar fadar Buckingham.
Ta rasu ne bayan ta shafe shekaru 70 a kan mulki.
Iyalanta sun taru a fadarta da ke Scotland bayan an rika nuna damuwa game da yanayin koshin lafiyarta ranar Alhamis.
Sarauniyar Ingila ta hau kan mulki ne a 1952 kuma ta ga sauye-sauye da dama.
Babban danta Charles, tsohon Yarima na Wales, ne zai jagoranci kasar wajen jimami a matsayinsa na sabon Sarki da kuma shugaban kasashe 14 na kungiyar Commonwealth.