Kungiyar ISWAP sun kai hari ga wasu kishiyar kungiyar ta’adanci wato mayakan Boko Haram.

Kungiyar ISWAP sun kai hari ga wasu kishiyar kungiyar ta’adanci wato mayakan Boko Haram da ke tserewa daga harin bama-bamai da sojoji suka kai a jihar Borno.

A baya dai an ruwaito cewa sojoji sun kashe mayakan Boko Haram sama da 200 da kwamandojin su a wani farmaki da sojoji suka kai musu da kuma yadda ambaliyar ruwa ta fatattaki wasu mahara da ta tilasta musu komawa gabas da karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.

Wasu daga cikin wadanda suka tsere sun nemi mafaka ne a kauyen Cina da ke karamar hukumar Bama a jihar amma an kai musu farmaki kamar yadda majiya ta bayyana.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, ya ce hare-haren da sojojin suka kai ya tilasta wa daruruwan ‘yan ta’adda da iyalansu barin sansanoninsu domin neman mafaka a wasu wurare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *