Daruruwan mayakan Boko Haram sun bar sansanonin su sakamakon ambaliyar ruwa.

Boko Haram Sun Shiga wani hali na fama da karancin abinci, makamai, bayan sun bar sansanonin su sakamakon Ambaliyar ruwa.

An tattaro cewa ambaliyar daga kogin Yedzaram ne ya tarwatsa sansanonin su da dama a Sheuri, a safiyar Lahadin da ta gabata.

Lamarin ya sa suka kaurace wa matsugunan su zuwa Iyakokin dajin Sambisa.

A baya dai, an ruwaito yadda ambaliya ta nutsar da mahara 70 sannan kuma sama da ‘yan ta’ada 200 da suka hada da kwamandoji biyar ne suka mutu sakamakon harin da sojojin Najeriya suka kai a makon da ya gabata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *