Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirinta na kara yawan kuɗin kira, tura sako da sayen Data a Najeriya.

Gwamnatin tarayyan Najeriya ta dakatar da shirinta na ƙara yawan Harajin da take karɓa daga kiran waya, Data da sauran ayyukan sadarwa.

Ministan Sadarwa na Najeriya Dr Isa Ali Pantami ne ya sanar da hakan a taron kaddamar da kwamitin kan kudaden haraji na bangaren tattalin arziki na dijital.

Pantami ya yi fatali da aiwatar da harajin, wanda ya bayyana a matsayin nauyi ga kamfanonin sadarwa.

Ya ce ba a tuntubi ‘yan majalisar dokokin kasar. Pantami ya kara da cesa shi da kan sa ya yi watsi da wannan manufa, ya kuma shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi watsi da ita duba da irin illar da za ta yi ga tattalin arzikin dijital.

A cewarsa, bullo da harajin fitar da kayayyaki a masana’antar sadarwa da fasahar sadarwa zai kawo cikas ga nasarorin da aka samu a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.