Sama da mutum 70 da ake zargin ‘yan Boko Haram ne ruwa yayi awon gaba da su a a wani rafi bayan luguden wutan da dakarun Operation Hadin Kai suka yi a jihar Borno, majiyoyi suka tabbatar.
An tattaro cewa, sojojin Najeriya tare da hadin guiwar kungiyar tsaron farar hula, JTF, sun halaka sama da ‘yan ta’addan Boko Haram 20 a kauyen Sheruri dake karamar hukumar Bama ta jihar Borno a ranar Alhamis.
Majiyoyi sun ce bayan farmakin Sheruri, wadanda suka tseren ruwa yayi awon gaba da su a rafin dake kusa da kauyen Dipchari dake karamar hukumar Bama a ranar Juma’a, Daily Trust ta ruwaito.
‘Yan ta’addan sun tafka mummunar asara, sun rasa rayukan sama da mayaka 70 a kusa da kauyen Dipchari. A halin yanzu da muke magana, mutane da yawa daga cikin mayakan babu su babu dalilinsu,” majiyar tsaro ta tabbatar”.
“Da safiyar yau wurin karfe 8:30 na safe suka yi jana’izar sama da mayaka 50 a kauyen Dipchari kuma suna cigaba da neman gawawwakin sauran ‘yan ta’addan”.
“Sun samo gawawwaki masu yawa daga rafin amma har yanzu akwai mayakan da ba a gani ba,” majiyar tace”.
Har yanzu babu takardar da ta fito a hukumance daga rundunar sojin Najeriya kafin rubuta wannan rahoton, amma jama’a da yawa daga yankin sun tabbatar da wannan cigaban.