A ranar Juma’a ne mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya gana da takwaransa na kasar Amurka, Kamala Harris a fadar White House da ke birnin Washington D.C kan muradun kasashen biyu.
Da yake jawabi a wajen taron, Osinbajo ya ce, dole ne kasashen biyu su ci gaba da yin aiki tare a matakai na kasashen biyu da na bangarori daban-daban, don tinkarar kalubalen da duniya ke fuskanta, da inganta zaman lafiya da tsaro, da magance cututtuka, da sauyin yanayi, da kuma matsalolin tattalin arziki.
Ya kuma yabawa dokar rage hauhawar farashin kayayyaki a Amurka.
Taron kasashen biyun ya zo ne bayan da Amurka ta fitar da “sabon hangen nesa” game da yankin kudu da hamadar Sahara a farkon watan da ya gabata.