Kotu Ta Wanke Tsohon Gwamna Jang Wanda Ake Zargi Da Zamba

Wata babbar kotun jihar da ke zamanta a Jos, babban birnin jihar Filato, a ranar Juma’a, ta sallami tsohon gwamnan jihar, Jonah Jang, tare da wanke shi daga zargin almundahana fiye da Naira biliyan 6.3 da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta yi masa.

Kotun da ke karkashin mai shari’a Christy Dabup ta kuma sallami wani tsohon mai karbar kudi a ofishin sakataren gwamnatin jihar Filato Yusuf Pam, wanda aka zarge shi tare da tsohon gwamnan.

A watan Maris din 2021 ne Jang ya roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yafewa wani tsohon gwamnan Filato, Joshua Dariye; tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame.

Majalisar kasa karkashin jagorancin shugaban kasa daga baya a watan Afrilun 2022 ta amince da yin afuwa ga masu laifi 159 da suka hada da Dariye da Nyame.

Kafin a sake su, Dariye yana zaman gidan yari na shekaru 10 bisa samunsa da laifin zamba N1.126bn yayin da Nyame ke zaman gidan yari na shekaru 12 da laifin karkatar da N1.64bn lokacin yana gwamnan Taraba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *