Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, ya jagoranci rantsar da sabbin kwamishinoni guda goma sha daya, a dakin taro na filin wasa na Sani Abacha dake kofar mata.
Gwamna ganduje ya hori sabbin kwamishinonin da suyi aiki tukuru bisa kwarewa domin sauke nauyin da aka dora musu inda ya sanar da ma’aikatun da aka tura su kamar haka;
1. Alh. Lamin Sani Zawiyya – Ma’aikatar kananan Hukumomin da Masarautu
2. Ya’u Abdullahi Yan Shana – Ma’aikatar Ilimi
3. Alhaji Ibrahim Dan azumi Gwarzo – Ma’aikatar kasafi da tsare-tsare
4. Abdulhalim Abdullahi Liman – ma’aikatar Raya karkara.
5. Dr. Jibril Yusuf rurum – Ma’aikatar Noma
6. Hon. Garba Yusuf Abubakar – ma’aikatar Ruwa
7. Hon. Adamu Abdu Panda – ma’aikatar kudi da cigaban tattalin arziki.
8. Hon. Sale Kausani – ma’aikatar gidaje da sufuri
9. Alh. Ali Musa Hamza Burum-burum – Ma’aikatar kula da yawun bude idanu da al’adun
10. Dr. Aminu Ibrahim tsanyawa – Ma’aikatar Lafiya
11. Alhaji Kabiru Muhammad – Ma’aikatar Aiyuka na Musamman.
Gwamnan yana tare da mataimakin sa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna da kuma dan takarar Mataimakin gwamna Alhaji Murtala Sule Garo da Shugaban Jam’iyya Alhaji Abdullahi Abbas da sauran shugabanni da dattijan Jam’iyya