Wike ga Shugaban PDP: “Girman kai da rashin godiya ba zai kai ka ko ina ba”.

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a ranar Alhamis, ya caccaki shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, kan nuna girman kai rashin nuna godiya bayan da aka taimaka masa wajen samun kujerar shugabancin jam’iyyar.

Wike ya kalubalanci Ayu da ya nuna kansa a matsayin mutum mai daraja da rikon amana ta hanyar cika alkawarin da ya dauka na cewa zai bar kujerar shugaban kasa idan yankin arewa ya fitar da dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar.

Ayu wanda ya fito daga jihar Benuwe da ke arewacin Najeriya a watan Oktoba ya ce zai bar kujerar shugabancin kasar idan yankin ya fitar da dan takarar shugaban kasa na PDP.

Amma a ranar Laraba, ya ce ba zai yi murabus ba. Tun da farko dai shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP Walid Jibrin da wani dan Arewa daga jihar Nasarawa sun amince cewa rashin adalci ne jam’iyyar ta samu dan takarar shugaban kasa da shugabanta na kasa daga yanki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.