Jami’ar Gombe ta janye daga yajin aikin ASUU

Majalisar gudanarwa ta Jami’ar Jihar Gombe (GSU) a ranar Alhamis ta umurci dukkan ma’aikatan makarantar da su koma bakin aiki cikin gaggawa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da sa hannun magatakardar jami’ar, Dr Abubakar Aliyu Bafeto.

Ya ce hukumar ta cimma wannan matsayar ne bayan taron gaggawa na ta karo na biyu da aka gudanar jiya, inda ya kara da cewa an samar da rajistar halartar ga malaman da ke son komawa aiki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *