Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da bullar cutar kyandar biri guda 53 da kuma cutar kwalara a jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar, Yakubu Danja ne ya bayyana hakan a wani taro da aka shirya wa ma’aikatan lafiya a Katsina, amma yace baa samu rahoton mutuwa ba.


Danja, wanda shi ya wakilci babban sakatare ma’aikatar Mustapha Kabir, ya ce an gano wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar ne daga samfurin wasu mutane 27 da ake zargin sun kamu da cutar aka aika dakin gwaje-gwaje.


A cewarsa, mutanen 27 da ake zargin sun fito ne daga kananan hukumomi 9 amma ba a bayyana jihar ba.
Kwamishinan ya bukaci mazauna yankin da su rika kiyaye ka’idojin tsafta a kodayaushe, kuma kada su yi jinkirin ziyartar cibiyoyin kiwon lafiya ko asibitocin da ke kusa idan sun lura da alamun rashin lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *