Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) zuwa jam’iyyar PDP.

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) zuwa jam’iyyar PDP a hukumance.

Wannan dai na zuwa ne bayan watanni uku da komawar Shekarau daga jam’iyyar APC zuwa NNPP.
Shekarau ya bayyana haka ne a ranar Litinin a gidansa da ke Mundubawa a Kano.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar da shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Iyorchia Ayu, da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP ne suka tarbe shi a hukumance.

Shekarau ya kuma ce ya rubutawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) takardar shelanta janyewa daga takarar sanatan Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar NNPP.

Sauran jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka halarci taron sun hada da dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar kuma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa; gwamnonin Sokoto da Taraba, Aminu Waziri Tambuwal da Darius Ishaku.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *