Kotu ta yi watsi da bukatar Gwamnatin tarraya na mika dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sandan ga Amurka.

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta yi watsi da karar da gwamnatin tarayya ta shigar, na neman a mika mata dakataccen mataimakin kwamishinan ‘yan sanda (DCP), Abba Kyari zuwa kasar Amurka domin yi masa shari’a kan laifin zamba ta yanar gizo.

Alkalin kotun, Mai shari’a Inyang Ekwo a lokacin da yake yanke hukuncin a ranar Litinin ya ce rashin amincewa da karar ta biyo bayan karar da babban lauyan gwamnatin tarayya Abubakar Malami da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA suka shigar.

Mai shari’a Ekwo ya gabatar da cewa sashe na 3 na dokar tuhume-tuhumen da ake yi a Najeriya ya haramtawa kasar mika masu laifi idan har ana tuhumar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *