Obasanjo: “Bani da wani dan takara da na fi a zaben 2023”.

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ba shi da wani dan takara da ya fi so a zaben shugaban kasa na 2023.

An ga Obasanjo ne a wani taro da Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, ya yi da gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers, a Landan, hakan ya sa majiyoyi suka ce shugaban na Najeriya yana goyon bayan takarar Obi.

Amma da yake magana a Minna, babban birnin jihar Neja, lokacin da ya kai wa tsohon shugaban kasa, Janar Abdulsalam Abubakar ziyara a ranar Lahadi, ya ce manufar sa ci gaban kasan ne, ba dan takara da ya fi so ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *