Rundunar sojin Najeriya ta kori wasu sojoji biyu bisa kashe Sheikh Goni Aisami Gashua, a jihar Yobe a makon da ya gabata. Sojojin da aka kora sun hada da Lance Kofur John Gabriel da Lance Kofur Adamu Gideon.
Muƙaddashin kwamandan rundunar 241 Reece da ke Nguru na Jihar Yobe, Laftanar Kanar Ibrahim Osabo, ya faɗa wa manema labarai cewa wani kwamatin haɗin gwiwa ne da aka kafa tsakanin ‘yan sanda da sojoji ya kama su da laifin.
Ya ce an kori sojojin ne kan tuhuma biyu da suka ƙunshi gazawa wajen gudanar da aikinsu da kuma ɓata sunan aikinsu.
Kanar Osabo ya ƙara da cewa za a miƙa su ga ‘yan sanda a birnin Damaturu don gurfanar da su a gaban kotu.