Za Mu Haɗa Kai Da Najeriya A Babban Zaɓen 2023 – Indiya

Indiya a matsayin kasar da ta fi kowacce kasa dimokuradiyya a duniya tana son hada kai da Najeriya domin samun nasarar babban zabe a shekarar 2023.

Karamin ministar harkokin waje da majalisar kasar Indiya, Vellamvelly Muraleedharan ne ya bayyana hakan a ranar Talatar nan a fadar shugaban kasa da ke Abuja, lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa, Ya je Abuja ne domin halartar taron kasuwanci tsakanin Najeriya da Indiya, kuma ya bayyana Najeriya a matsayin “cibiyar huldar mu da Afirka.”

Ya ce Buhari ya kasance “cancantancen tsohon dalibin kwalejin tsaron mu.”

An ruwaito cewa, Muraleedharan, wanda ya isar da gaisuwa Furaministan Indiya Narendra Modi, ya ce Najeriya da Indiya suna da kyakkyawar alaka ta fuskar kasuwanci, tsaro, ilimi da dai sauransu.

Buhari ya sauka a fagen tunawa da horon da ya yi na shekara guda a Indiya a matsayin jami’in soji a Kwalejin Tsaron da ke Wellington, ya tuna da ziyarar da ya kai a shekarar 1973.

Ya ce: “Wannan kwarewa ce mai kyau. Ina tsammanin ni laftanal kanal ne a lokacin, kuma na yi shekara guda a Indiya. Mun yi balaguro kuma mun haɗu da mutanen duniya daga ƙasashe daban-daban. Ya zama wani bangare na nasarar da na samu a aikin soja.”

Shugaban ya ce Indiyawa ne suka kafa makarantar horas da sojoji ta Najeriya.

Ya ce kasashen biyu na da tsayuwar alaka ta fuskar tattalin arziki da siyasa da kuma ta fuskar tsaro.

Buhari ya ce dole ne Najeriya da Indiya su ci gaba da kulla dadaddiyar alakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Kamar yadda Kwamishinan hukumar ya shaida, ya ce wannan na zuwa ne a wani Mataki na Firaministan Kasar Indiya Narendra Modi na taimakawa al’ummar duniya fita daga fadawa wannan cuta.

Kazalika kuma hakan na daga cikin yunkurin kara yaukaka dangantaka daje tsakanin kasashen biyu kamar yadda aka sani tun tale-tale.

Leave a Reply

Your email address will not be published.