Dakarun sojoji a karamar hukumar Bama a Jihar Borno, sun kashe mayakan Boko Haram 6.

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojoji a karamar hukumar Bama a Jihar Borno, sun kashe mayakan Boko Haram shida a wani samame da suka kai wata kasuwa ta haramtacciyar hanya da ‘yan ta’addan suka kafa.


Sojojin tare da hadin guiwar rundunar hadin guiwa ta Civilian CJTF sun kai farmaki kan haramtacciyar kasuwar wadda aka fi sani da Kasuwar Daula a kauyen Bararam da ke garin Bama a ranar Larabar da misalin karfe 11 na safe, inda suka kai farmakin.


A lokacin da aka samame kasuwar, inda sojojin kasuwar kamar yadda wani masani kan yaki da ta’addanci kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, Zagazola Makama ya bayyana.


Makama ya bayyana cewa ‘yan ta’addar sun bude wuta ne bayan da suka ga sojojin, inda ya kara da cewa sojoji sun kashe shida daga cikinsu.


A cewarsa, a kasuwar ana sayar da kayayyaki irin su masara, wake, gishiri, kwayoyi, da kuma man fetur ga ‘yan ta’addar.


Wadanda ake zargin, a cewarsa, an kai su hedikwatar sojoji da ke Bama domin gudanar da cikakken bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *