Rundunar sojin Najeriya za ta gudanar da binciken jami’an sojoji 2 kan kisan Sheikh Goni Gashua.

Rundunar sojin Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike bayan an kama wasu jami’an sojoji biyu kan kisan wani malamin addinin Islama a jihar Yobe, Sheikh Goni Gashua.

A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Kennedy Anyanwu ya sanyawa hannu, rundunar ta riga ta tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar Yobe domin bayyana sunayen ‘jami’an sojin da ake zargi.

“Bugu da kari kuma, Sashen ya kafa wani kwamitin bincike domin bankado al’amuran da suka shafi wannan lamari mara dadi”.

“A karshen binciken, za a sa sojoji su fuskanci fushin dokokin soja da na farar hula.”

“Wannan lamarin abin bakin ciki ne matuka ganin yadda bangarorin suka nuna halin ko in kula game da saba dokoki da ka’idojin aiki na sojoji.”

“Saboda haka, sashen na fatan jajantawa iyalan wanda abin ya shafa da kuma mutanen jihar Yobe nagari tare da yin alkawarin cewa za a yi adalci a kan haka.”

Kisan Sheikh Goni Gashua.

Gidan Talabijin na Channels ya bada labarin kashe Sheikh Goni Aisami-Gashua a ranar Asabar.

An ce malamin ya taso ne daga Gashua zuwa Kano a cikin wata motar safa da maharan suka bi shi.

Wasu mazauna Gashua sun shaida wa gidan talabijin na Channels cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safe a Jajimaji mai tazarar kasa da kilomita 30 daga Gashua, mahaifar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim, a wata tattaunawa ta wayar tarho da wakilinmu, ya ce an kama wadanda ake zargin dauke da bindigogi kirar AK-47, kuma suna hannun ‘yan sanda a yau.

Gashua dai na daya daga cikin al’ummar jihar da suka fi zaman lafiya, hatta a lokacin da ake fama da rikicin Boko Haram.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *