Hukumar kula da gidajen rediyo da talabijin NBC ta soke lasisin gidajen Talabijin mai zaman kansa na Afrika (AIT), da Silverbird Television (STV), da wasu gidajen rediyo 50.
Da yake zantawa da manema labarai a Abuja ranar Juma’a, Darakta Janar na Hukumar, Malam Balarabe Shehu Ilelah.
Ya ce tashoshin da lamarin ya shafa na bin bashin kimanin Naira biliyan 2.6, wasu daga cikin su tun shekarar 2015.
A cewarsa, a watan Mayu, hukumar ta buga sunayen tashoshin da har yanzu ba su sabunta lasisi ba, ta kuma ba su makwanni biyu su yi hakan ko kuma a kwace musu lasisi.
Ya ce bayan wata uku da wallafar wasu gidajen rediyon har yanzu ba su biya bashin da ake bin su ba wanda ya sabawa dokar CAP N11, Dokokin Tarayyar Najeriya, 2004, musamman sashe na 10 (a) na jaddawalin dokar na uku.
Da yake sanar da janye lasisin, Ilelah ya umurci tashoshin da abin ya shafa da su dakatar da ayyukansu cikin sa’o’i 24.
Ya kuma yin kira ga duk tashoshin da ba su sabunta lasisin su ba a halin yanzu da su yi hakan cikin kwanaki 30 don kauce wa takunkumi.