Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana Janal Ibrahim Badamasi Babangida a matsayin jigo na tsarin dimokuradiyyar Najeriya.

Buhari wanda ya bayyana haka a sakon  taya murnar cika shekaru 81 a duniya da ya aikewa tsohon shugaban ya kuma kara da cewar tarihin siyasar wannan kasa ba zai manta da irin gudumowar da Ibrahim Badamasi Babangida ya bayar ba.

Sakon wanda ke dauke da sa hannun mataimakin na musamman ga Shugaban kasa akan labarai Femi Adesina ya kuma Yan uwa da abokan arziki shugaban murnar tare da adduar samun karin lafiya da nisan kwana ga Janal Ibrahim Badamasi Babangida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *