Majalisar dokokin jihar Katsina ta kira yi gwamnatin jihar Katsina data gaggauta gyara hanyar Ƙanƙara zuwa Sheme da kuma hanyar Yankara zuwa Faskari da ta wuce har zuwa Marabar Ƙindo.

Majalisar dokokin jihar Katsina ta gabatar da wani ƙuduri kan gwamnatin jihar Katsina ta gyara hanyar da ta taso daga garin Ƙanƙara ta dire zuwa cikin garin Sheme da kuma hanyar da ta taso daga cikin garin Yankara ta shiga Faskari ta yi Maigoro ta dire har zuwa marabar Ƙindo.

Kudurin na hadin guiwa da ɗan majalisar mazabar Faskari Hon Engr Shehu Dalhatu Tafoki, da na Ƙanƙara Hon Ya’u Garba Mabai da kuma na karamar hukumar Sabuwa Hon Ibrahim Kaka Machika suka gabatar, sun bayyana muhimmancin gyaran hanyar musamman duba da yadda yankunan ke fama da matsalolin tsaro.

Lokacin da yake gabatar da kudirin Hon Shehu Dalhatu Tafoki ya ce “Gyaran hanyar na da matukar mahimmanci duba da matsalolin tsaro da yankin yake fama da su, saboda haka gyara wannan hanya zai taimaki al’ummar wadannan yankuna musamman akan matsalar tsaro da ta addabesu.”

Kamar yadda majiyar Katsina Media Post News ta ruwaito mana, bayan kammala muhawara game da batun sauran yan majalisar sun aminta da kudurin gyaran hanyoyin, inda Kakakin majalisar Rt. Hon Tasi’u Maigari Zango ya umurci akawun majalisar da ya shigar da koken cikin wasikar da za a aika wa majalisar zartarwar jihar Katsina domin zartar da koken

Leave a Reply

Your email address will not be published.