Hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya haura zuwa 19.64% a watan yuli.

Kididdigar farashin kayayyaki ta kasar (CPI), wacce ke auna canjin farashin kayayyaki da ayyuka, ya kai kashi 19.64 a watan Yulin 2022 daga kashi 18.60 da aka samu a watan da ya gabata.

Wannan na nufin karin kashi 1.82% na wata-wata, a cewar rahoton (CPI) na Yuli 2022 da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar ranar Litinin.

NBS ta kara da cewa “A duk wata-wata, hauhawar farashin kayayyaki a cikin watan Yulin 2022 ya kasance 1.817 %, wanda ya kai 0.001% sama da adadin da aka samu a watan Yuni 2022 (1.816%),” in ji NBS.

Canjin kashi a matsakaicin CPI na tsawon watanni goma sha biyu da ya ƙare Yuli 2022 akan matsakaicin CPI na tsawon watanni goma sha biyu da suka gabata shine 16.75%, yana nuna haɓaka 0.46% idan aka kwatanta da 16.30% da aka rubuta a Yuli 2021.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *