Gwamnatin Tarayya ta yi asarar kudaden shiga sama da Naira biliyan uku tun bayan da ta dakatar da jigilar jirgin kasa tsakanin Abuja zuwa Kaduna.

Kullum ana asarar Naira miliyan 21.6 na tikitin jirgin kasan, a tsawon kwana 140 tun bayan harin ’yan ta’adda a kan jirgin kasan a ranar 28 ga watan Maris, 2022.

Rufe harkokin jirgin kasan ya haddasa rufe harkokin kasuwanci da sauran harkokin neman abinci da mutane ke yi a wurin.

An dakatar da jigilar jirgin kasan ne bayan harin bom din da ’yan ta’adda suka kai wa jirgin da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna dauke da mutum 970.

Maharan sun kashe kimanin 10 daga cikin fasinjojin, suka yi garkuwa da wasu 60, baya ga wadanda suka jikkata a sakamakon harin.

A sanadiyyar haka ne Hukumar Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta dakatar da harkokin jirgin sai abin da hali ya yi.

’Yan ta’addan sun sako wasu daga cikin fasinjojin bayan an biya kudaden fansa, amma har yanzu akwai wasu a hannunsu.

A halin da ake ciki, NRC ta ce ba za ta ci gaba da gudanar da harkokin jirgin kasan Kaduna-Abuja ba har sai an sako duk fasinjojin da aka yi garkuwa da su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *